
Jiddah (UNA) - Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan sake dawo da mummunan harin soji da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan shahidai, da jikkata wasu da kuma bacewar wadanda akasarinsu yara da mata da kuma tsofaffi ne.
Kungiyar ta kuma yi kira ga al'ummar kasa da kasa, musamman ma kwamitin sulhu na MDD, da su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu, ta hanyar aiwatar da shirin dakatar da kai hare-haren wuce gona da iri na Isra'ila, da bude mashigin ruwa, da tabbatar da isar da kayan agaji ga dukkan sassan zirin Gaza, da fuskantar yunkurin mamaye Palasdinawa, da samar da kariya ga al'ummar Palasdinu.
(Na gama)