A yau ne ofishin yada labarai na lardin Yunnan na kasar Sin, tare da hadin gwiwar karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Jeddah, da ofishin kula da harkokin waje na lardin, suka shirya wani taron manema labarai mai taken "Bi sawun Zheng He zuwa kasar Saudiyya."
Taron dai na da nufin nuna zurfafa dangantakar tarihi tsakanin kasar Sin da yankin Larabawa, inda ake tunawa da tafiye-tafiyen da shahararren ma'aikacin jirgin ruwa na kasar Sin Zheng He a karni na 15 ya yi. An haife shi a birnin Yunnan, ya jagoranci wani jirgin ruwa da ya isa Tekun Bahar Maliya, inda daga nan ne ya tashi zuwa Jeddah da garuruwan Makka da Madina, ya zama wata gada ta hanyar sadarwa ta al'adu da kasuwanci tsakanin kasar Sin da kasashen musulmi.
Bikin ya zo daidai da cika shekaru 620 na ziyarar Zheng He da kuma cika shekaru 35 da kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Saudiyya, wanda ya kara ba da wani matsayi na musamman ga bikin. Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin inganta mu'amalar al'adu da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, tare da yin la'akari da abubuwan tarihi da suke da su.
Ana yi wa Zheng He kallon daya daga cikin fitattun mutane a tarihin zirga-zirgar jiragen ruwa a duniya, inda ya jagoranci tafiye-tafiyen teku guda bakwai da suka taimaka wajen inganta tattaunawa tsakanin wayewa da karfafa dankon zumunci tsakanin al'ummomi.
(Na gama)