masanin kimiyyar

Saudiyya ta bayyana kakkausar suka da Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Riyad (UNA/SPA)- Masarautar Saudiyya ta bayyana kakkausar suka da kuma yin Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kaiwa kan ‘yar uwar jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadanda ke dakushe ‘yancinta da tsaronta da kuma keta dokokin kasa da kasa.
Yayin da Masarautar ta yi Allah wadai da wadannan munanan hare-hare, ta kuma tabbatar da cewa kasashen duniya da kuma kwamitin sulhu na da alhakin dakatar da wannan ta'asa cikin gaggawa.
(Na gama)

Labarai masu alaka

Je zuwa maballin sama