
Geneva (UNA/SPA) – Ministan lafiya na kasar Saudiyya Fahd bin Abdulrahman Al-Jalajel ya gudanar da taron kasashen biyu a yau tare da ministan lafiya na kasar Siriya Musab Nazzal Al-Ali, a wani bangare na halartar taron kolin lafiya na MDD karo na 78 na hukumar lafiya ta duniya a hedikwatar MDD dake Geneva.
Taron ya tattauna kan kalubale daban-daban da tsarin kiwon lafiyar kasar Siriya ke fuskanta da kuma damar yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tinkarar wadannan kalubale.
(Na gama)