
Riyad (UNA/SPA) – Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana Allah wadai da tofin Allah tsine da kakkausar murya kan harin kunar bakin wake da aka kai a sansanin soji na Zero Damayo da ke Mogadishu, babban birnin Tarayyar Somaliya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata wasu da dama.
Masarautar ta jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, da gwamnati da al'ummar Somaliya, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Masarautar ta sake jaddada kin amincewa da duk wani nau'in ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, da kuma hadin kai da Somaliya da 'yan uwanta a wannan lamari mai raɗaɗi.
(Na gama)