
Makkah (UNA) – Kungiyar kasashen musulmi ta duniya ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da keta dokokin kasa da kasa da ka’idojinta, ciki har da sanarwar da ta yi dangane da kutsawa da iko da yankin zirin Gaza da kuma yankunan Palastinawa.
A cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar kungiyar ta fitar, mai girma babban sakataren kungiyar kuma shugaban kungiyar malaman musulmi Sheikh Dr. Muhammad bin Abdulkarim Al-Issa, ya yi Allah wadai da wannan dabi'a ta dabbanci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi, tare da yin watsi da duk wani yunkuri da take yi na fadada ayyukanta, wanda ya saba wa kudurin kasa da kasa da kuma kawo cikas ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da adalci a yankin.
(Na gama)