
Geneva (UNI/WAFA) – Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa, a kullum ana kashe kananan yara Palasdinawa 35 a zirin Gaza, sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke yi.
Kakakin hukumar UNICEF James Elder ya fada a jiya Juma’a yayin taron manema labarai na mako-mako da aka gudanar a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva na kasar Swizalan, cewa bisa ga kididdigar likitocin, an kashe kananan yara 15 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023..
Ya bayyana cewa: “Wannan yana nufin kashe yara 35 a kowace rana tsawon watanni 14".
(Na gama)